Sunday, May 5, 2019

YANDA AKE GANE TSAYUWAR WATA


TAMBAYA:YAYA AKE GANE TSAYUWAR WATA

AMSA:WATAN RAMADAN YANA TABBATA NE DA ZARAR ANGA JINJIRIN WATA KO WATAN SHA'ABAN YA CIKA  KWANA TALATIN . DOMIN HADISI YA TABBATA DAGA ABU HURAIRAH (RA) CEWA MANZON ALLAH (SAW) YACE:
    Kuyi azumi domin ganinsa (wato Ramadan) kuma Ku sha ruwa domin ganinsa (wato Shawwal) idan WATAN ya faku agare Ku (Baku ganshiba),to Ku cika sha'aban kwana talatin.
  Sahihul bukhari(1909)da sahih Muslim (1081)
Daga littafin fatawoyin azumin WATAN Ramadan na shaikh abdulwahab abdullahi

Domin samun cikakkun fatawoyi akan ma'salolin addini said a nememu a shafinmu na zinariyah.blogspot.com


No comments:

Post a Comment