Friday, May 10, 2019

Hukuncin Wanda ya yima matarshi kiss da azumi


TAMBAYA: MENE HUKUNCIN WANDA YA KALLI MATARSA BA TARE DA YA TABATA BA,SAI YA FITAR DA MANIYYI?


AMSA:hakika Wanda ya samu Kansas a irin wannan halin zai cigaba da azuminsa ,kuma babu kome akansa.dalili akan haka na cikin hadisin jabir  ibn zaid (ra)yace:Wanda ya kalli mace ya fitar da maniyyi, yaci gaba da azuminsa, babu komai akansa.
   Imam al-shafi'i (babban almajirin imam  malik), da imam al-thauri da imam al-auza'i duk sun tafi akan cewa babu wani dalili da yazo akan cewar fitar da maniyyi kadai yana karya azumi ,ba tareda jima'i ba amma idan jima'i ne, koko an fitar da maniyyi ko ba'a fitar ba ,yana karya azumi ,kuma sai anyi kaffara .haka kuma Wanda ya sumbaci matarsa (kiss) har ya fitar da maziyyi shima azuminsa yana nan. Wannan shine zance mafi rinjaye.
Sai dai wasu daga cikin malaman mazhabar malikiyyah sun ce,fitar da maniyyi ta hanyar kallo ko runguma yana karya azumi, kuma akwai ramuwa da kaffara a kai. Amma idan maziyyi ne kawai akwai ramuwa ba tareda kaffara ba.sun kafa hujjar cewa abinda ake bukata a jima'i shine fitar maniyyi. Saboda haka fitar maniyyi ta wannan hanya daidai yace da jima'i.
  Amma sauran many an malamai sunyi masu raddi cewa hukuncin da nassi yazo dashi ya ambaci jima'i ne kawai ,ba fitar da maniyyi ba. Sannan suka kara da cewa idan da mutum zai yi jima'i ba tareda ya fitar da maniyyi ba ,ai zai rama azumi ne kuma yayi kaffara . haka kuma da ace fitar da maniyyi ne kawai ake lura da shi ,sai ace me bacci ma idan yayi mafarki ya fitar da maniyyi, sai yayi kaffara.
  (Sharh sahihul bukhari ,na ibn battal al-mālilī, 4 /52-56)
  Daga littafin fatawoyin azumin Ramadan na abdulwahab abdullah
Domin samun cikakkun fatawoyin musulunci sai a nememu a shafin mu na zinariyah . blogspot. Com

No comments:

Post a Comment