Wednesday, May 15, 2019

FASSARAR LITTAFIN HALITTA AYYUKAN BAYI NA AL-IMAMUL BUKHARIY

FASSARAR LITTAFIN HALITTA AYYUKAN BAYI NA AL-IMAMUL BUKHARIY

Na Babban Malami Dr, Kabir Abbakar  Asgar
Daya daga cikin daliban Sheikh  mallam Auwal Adam Albanin Zaria

From our blog www.zinariyah.blogspot.com 
Facebook page Facebook.com/zinariyah

Babin da ke bayani akan batutuwan malamai akan masu lalata siffofin Allah.
1- Daga Sufyanu dan Uyainah, y ace “Na riski malamanmu tun kafin shekaru 70, irin su Amr dan Dinar suna cewa Qur’ani zancen Allah ne ba halitta ba”
2- Daga Sulaiman Al-Qariy y ace: “Na ji Sufyan As-thauriy yana cewa Hammad dan Abu Sulaiman ya ce da ni ka shaida wa baban wane mushirikin nan cewa ba ni ba shi. Saboda ya kasance yana cewa Al-qur’ani halitta ne”
3- Daga Abdurrahman dan Muhammad dan Habibah, daga babansa daga kakansa ya ce: “Na halarci sallar idin babbar sallah a garin Wasit tare da Khalid dan Abdullahi Al-Qasariy. Da ya idar da sallah sai ya ce  ku koma gidajenku ku yanka layyarku, ina fata Allah ya karba muku. Ni kam zan yi layya ne da Ja’adu dan Dirham. Ja’adu na riya cewa wai Allah bai riki Ibrahim a matsayin babban masoyi ba. Kuma wai Allah bai yi magana da Musa ba. Allah ya daukaka daga abin da Dan Dirham ya ke fadi”. Sannan ya yanka shi
4- Baban Abdullahi ya ce: “Qutaiba ya ce na sami labarin Jahamu ya koyi karatu a wajen Ja’adu dan Dirham”.
5- Abu Zakariyya, Yahya dan Yusuf ya ce “Muna zaune tare da Muhammad Dan Idris sai wani ya zo ya tambaye shi cewa me zai ce game da mutanen da cewa Al-Qur’ani halitta ne? sai ya ce: “Yahudawa ne?” Sai mai tambayar ya ce “A’a” Sai ya ce” “Kiristoci ne?” ya ce: “a’a” Ya ce: “To maguzawa ne?” ya ce: “a’a”. sai ya ce: “To wadanne irin mutace ne?” sai ya ce: “Musulmai ne” Sai malam ya ce: “A’a, wadannan ba musulmai ba ne, zindiqai ne. Wanda duk ya ce Al-Qur’ani halitta ne ya ce Allah halitta ne. Suna so ne su ce (بسم الله الرحمن الرحيم) halitta ne. Allah ba halitta ba ne, Arrahman ba halitta ba ne. Arraheem ba halittta ba ne. Wannan shine tushen zindiqance. Wanda duk ya fadi wannan magana Allah ya tsine masa albarka, kar ku yi zamantakewa da su. Kar ku yi auratayya da su".
6- Wahabu Dan Jareer yana cewa: “Jahamawa zindiqai ne, suna so ne su su ce Allah bai daidaita akan al’arshi ba
7- Jazeedu Dan Haroon ya yi rantsuwa da Allah ya ce: “Na rantse da Allah wanda babu sarki sai shi duk wanda ya ce Al-Qur’ani halitta ne zindiqi ne, za a umurce shi ya tuba, in ya tuba shi kenan, in kuwa ya ki sai a kashe shi”.
8- An bai wa Abubakar Dan Ayyash labarin cewa wasu mutane a garin Baghdad suna cewa Al-Qur’ani halitta ne. Sai ya ce: “Su waye masu wannan maganar? Allah ya tsine musu. Duk wanda ya ce Al-Qur’ani halitta ne kafiri ne kuma zindiqi. Kar ku dinga zama da su”.
9- Sufyan Atthauriy ya ce: “Wanda ya ce Al-Qur’ani halitta ne kafiri ne”
10- Hammad Dan Zaid ya ce: “Al-Qur’ani maganar Allah ne, Jibrilu ne ya sauko masa da shi, so suke su yi su ce babu Allah a sama”.
11- Ibn Muqatil ya ce: “Na ji Ibnul Mubarak yana cewa: “wanda duk ya ce (إننى أنا الله لا إله إلا أنا) halitta ne kafiri ne. Bai dace mutum ya yi irin wannan ba”. Sannan sai ya ce: “Ba na fadin zance irin na Jahamu, zancen nan da yai kama da na shirka. Ba na fadin cewa Allah ya yi watsi da halittunsa, ya bar su da shaidan, ko fir’auna duk da kangarewarsa, bai taba fadin irin wannana maganar ba”.
12- Ibnul Mubarak ya ci gaba da fadin cewa: “Kar ka fadin irin zancen Jahamiyyah da suke cewa Allah ya na ko ina. Lallai Allah ya daidaita a kan Al-Arshinsa”. Sai aka ce masa: “Me za mu kudurce game da Ubangijinmu?” Sai ya ce: “A sama, birbishin Al-Arshinsa” Sai ya ce da waninsu: “Kana zaton ka wofanta daga Shi ne?” Sai ya kasa amsa masa. Sai ya ce: “Wanda ya ce (لا إله إلا الله) halitta ce, to ya kafirta. Mu muna iya ba da labarin Yahudu ko Nasara amma ba ma iya hakaito zantukan Jahamawa saboda muninsu”
13- Mu’awiya Dan Ammar ya ce: “Na ji Ja’afar Dan Muhammad yana cewa Al-Qur’ani maganar Allah ce ba halitta ba ne”
14- Saidu Dan Amir yana cewa: “Maganar Jahamawa ta fi ta Yahudu da Nasara muni. Domin kuwa Yahudu da Nasara da sauran masu bin addinan sama sun hadu akan cewa Allah ya daidaita a kan Al-Arshi amma su Jahamawa sun karyata”
15- Daga Ibn Shauzab: “Jahamu Dan Safwan ya daina Sallah tsawon kwanda arba’in saboda ya yi jayayya da Samaiyyawa sun sanya masa shakka game da Sallah”
16- Abdul-Azeez Dan Abu Salamah ya ce: “Lallai zancen Jahamu zance ne maras ma’ana. Ya tsara zancen ne ba-kai-ba-gindi. Ya gina shi ne ba bisa tushe ba. Kuma dama can ba a taba lissafa Jahamu a cikin malamai masana ba”
17- An taba tambayar Jahamu Dan Safwan game da hukuncin mutumin da ya saki matarsa kafin ya tare da ita, sai ya ce: “Za ta yi idda” Ka ga ya saba wa littafin Allah saboda jahilcinsa. Allah ya ce: “Ba ku da iddar da za ku lissafa akan su''.
18- Aliyu ya ce: “Wadanda suka ce Allah yana da da sun fi kafirci fiye da wadanda suka ce Allah ba ya Magana”
19- Ya ce: “Ka kiyayi zantukan Bishir Al-Mareesiy shi da jama’arsa, lallai zancen su yana jawo zindiqanci. Na tattauna da malaminsu Jahamu, ya nuna min shi bai yarda akwai Allah a sama ba”
20- Ismai’ilu dan Abu-Uwais ya kasance yana kiransu da “zindiqan Iraq”. An tamabaye shi cewa: “Ka taba jin wani na cewa Qurani halitta ne?” sai ya ce: “Wadannan zindiqan Iraq ne, haqiqa na gudu na bar Bagdad na koma Sham lokacin da na ji Abbas yana fadin irin wannan magana a Bagdad don na guje wa maganar”.
21. Aliyu dan Hassan ya ce: “Na ji Ibn Mus’ab yana cewa Jahamiyya sun kafirta ta fuskoki da yawa. Sun ce Aljanna za ta kare, alhalin Allah yana cewa (Lallai wannan arzikinmu ne ba ya karewa) {Suratu Saad, 4}. Wanda duk ya ce za ta kare to ya kafirta. Wanda duk ya ce arzikinta zai yanke to ya kafirta saboda Allah ya ce (abin cin ta madawwami ce da inuwarta) {Suratur Raad, 35}. Wanda duk ya ce ba za ta dawwama ba ya kafirta saboda fadin Allah (Ba abin yankewa ba ce kuma ba abin hanawa ba) {Suratul Waqia, 33}. Wanda duk ya ce mai yankewa ce ya kafurta saboda fadin Allah (kwauta ce ba mai yankewa ba) {Suratu Huud, 108}. Ya ce ku je ku ce na ce kafirai ne, matansu sakakku ne.
22. Ibun Mubarak ya ce daga Ma’amar “Fadin Allah (Kuma kalmarsa ce da ya wurga ta akan Maryam) {Suratun Nisa’i, 171} Ya ce ma’anarsa zancensa na ZAMO SAI YA ZAMO”.
23. Ibn Ma’adan ya ce “Na tambayi Al-Thauriy ma’anar (Kuma yana tare da ku a duk inda kuke) {Suratul Hadeed, 4} sai ya ce DA ILIMINSA”
24. Abul Walid ya ce: “Na ji Yahya dan Saidu yana cewa –a yayin da aka ba shi labarin masu cewa Al-Qur’ani halitta ne- sai ya ce  ya za ku yi da fadin Allah (KA CE SHINE ALLAH GUDA DAYA?). ya za ku yi da fadin Allah (LALLAI NINE ALLAH WANDA BA ABIN BAUTA SAI SHI?)”.
25. Affan ya ce: “Wanda ya ce (قل هو الله أحد) halitta ne to ya fita daga musulunci”.
26. Aliyyu dan Abdullahi ya ce: “Al_Qur’ani zancen Allah ne, wanda ya ce halitta ne ya fita daga addinin musulunci, bai halasta a bi shi sallah ba”.
27. Waki’u ya ce: “Wanda yai musun hadisin Isma’il daga Qais daga Jareer akan ganin Allah to bajahame ne ku kiyaye shi”.
28. Abul Waleed ya ce: “Wanda ya ce Al-Qur’ani halitta ce ya fita daga musulunci. Wanda bai qudurce a zuciyarsa cewa Al-Qur’ani zancen Allah ba ne ya fita daga musulunci”.
29. Baban Abdullahi ya ce: “Na nazarci zantuttukan Yahudawa da Kirista da Majusawa, amma ban ga wanda ya kai kafircin Jahamawa da bata irin ta su ba. Don haka, ina kallon wanda ya ki kafirta su ne a matsayin jahili wanda bai san irin abin da suke fadi ba”.
30. Abdurrahman dan Affan ya ce: “An ambaci mas’alar da aka daki Bishiru  akanta a majalisin Malam Sufyan dan Uyainah sai ya mike cikin fushi sannan ya ce: Kai jama’a! Al-Qurani maganar Allah ce, haka na riski malamai suna fadi; Su Amru dan Dinar da Ibnul Munkadir da Mansoor da Al-A’amash da Mis’aru dan Kidam. Dukkaninsu sun tsoratar akan bidioin Mu’utazilah da Rafidah da Qadariyyah kuma sun yi umarni da a kauracewa wadannan bidioi. Sannan sai ya ce a iya saninmu Al-Qur’ani maganar Allah ne, wanda duk ya fadi wani abu sabanin haka Allah ka tsine mishi albarka. Wannan zancen ai irin na Kirista ne, ku daina zama da masu fadin irin wannan zancen, ku daina sauraron su.”
31. Abdullahi dan Muhammad ya ce: “An ambaci Mariseey sai na ji Ibn Uyainah ya ce: Me ‘yar dabbar nan ta ke fadi? Me ‘yar dabbar nan ta ke fadi? (watau yana mai yi ma Mariseey din ishizaa’i) Sannan ya ce: Na ji Muhammad Dan Ubayd yana cewa: Wannan wulakantaccen (wato Bishir) ya zo yana tambaya ta wani hadisi. Wallahi ko na sani ba zan fada masa amsar ba”.
32. Daga Abdullahi Dan Mas’ud ya ce: “Allah bai halicci sama ko kasa ko aljanna ko wuta da suka kai darajar fadin sa (الله لا إله إلا هو الحي القيوم) ba”.
33. Sufyan ya fassara maganar da cewa: “Watau komai halitta ne amma ban da Al-Qur’an. Kuma maganar Allah ta na sama da halittarsa. Saboda yana ce wa abu zamo kaza sai ya zamo din. Ba wani abu da zai zam sama da kalmar da Allah key in halitta da fadinta. Al-Qur’ani maganar Allah ne”.
34. Zuhair Assijistaniy ya ce: “NA Sallamu Dan Abu Mudee’i yana cewa Jahamawa kafirai ne”.
35. Abdulhameed ya ce: “Jahamu Dan Safwan ya kafirce wa Allah Ubangiji mai girma”.
36. Wakee’u ya ce: “Wadannan mutane (watau Jahamiyya da Murji’ah) sun zo da bidi’a. Jahamiyya kafirai ne. Marisiy Bajahame ne.” Sannan sai ya ce: “Kun san yadda aka yi suka kafirta?” Sai ya ce: “Murji’ah suna cewa wai imani magana ce ba tare da aiki ba. Wannan magana bidi’a ce. Duk wanda ya ce Al-Qur’ani halitta ne ya kafirce wa abin da Allah ya saukar wa Annabi Muhammadu (SAW), za a nemi ya tuba in yaki a kashe shi.
37. Wakee’u ya ce: “Allah ya tsine wa Bishir” sannan ya tambaya ya ce: “Hala dai Bishir Bayahude ne ko Banasare?” Sai wani ya ce: “Babansa ya kasance Bayahude ne ko Banasare”. Sai Wakee’u ya ce: “Allah ya tsine masa shi da mabiyansa. Al-Qur’ani maganar Allah ne” Sannan Wakee’u ya dosa tafa hannayensa (yana mamaki).
38. Sannan ya ce: “Mummunar aqida ta zo Bagdad. Wannan da ake ce wa Marisiy a neme shi da ya tuba in ya ki a kashe shi.”
39. Yazeedu Dan Haroon ya ce: “Haqiqa na yi iya kokarin da zan iya wajen zuga mutanen Bagdad don su kasha Bishir. An taba ba ni labarin wata (muguwar) magana da ya fada, sai da na kwana uku ina jin nauyin ta a gadon bayana.”
40. Aliyu Dan Abdullahi (Al-Madeeniy) ya ce: “Manufar (Bishir) ita ce ya shigar da mutane cikin (aqidarsa) ta kafirci.”
41. Ubayd Dan Aisha ya ce: “Mu ba ma sallah a bayan wanda ya ce Al-Qur’ani halitta ne. Wanda ya fadi haka ba shi da mutunci a idonmu. Idan yana sallah don ya kare kansa to shi ya jiyo. Amma dai ni na fi gane wa kowa a kiyaye shi a guje masa. Don cewa suke yi ba Allah!”
42. Sulaiman Dan Daud Al-Hashimiy da shi da Sahal Dan Muzahim suna cewa; “Wanda duk yai sallah a bayan mai cewa Al-Qur’ani halitta ne to ya sake sallah”.
43.  Ibn Al-Aswad ya ce na ji (Abdurrahman) Dan Mahadiy yana fada wa Yahya Dan Saidu cewa: “Da a ce akwai dangantar jini tsakanina da Jahamu ba zan halasta wa kaina gadon sa ba.
44. Ibn Mahadiy ya ce: “Da zan ga mutum akan gada yana cewa Al-Qur’ani halitta ne in ina da takobi a hannuna da ba sara masa a wuya”.
45. Yazeedu Dan Haroon ya ce: “Bishir bai kai darajar jakina ba”.
46. Baban Abdullahi (Al-Bukhariy) ya ce: “Sallah a bayan Bajahame ko Rafidiy (Dan Shia mai tsine wa magabata) ba shi da bambamci da sallah a bayan Bayahude ko Nasara. Bai halasta ai musu sallama ba, bai halasta a je gaishe su ba in ba su da lafiya, bai halasta a yi auratayya da su ko a sa su shaidar aure ba. Kuma bai halasta a ci yankan su ba”.
47. Abdurrahman Dan Mahadiy ya ce: “Jahamiyyanci da Rafidanci wasu addinai ne masu zaman kan su.
48. An bai wa Ibn Ubayd labarin cewa an tambayi Bishir game da farkon halitta da ma’anar fadin Allah (Kadai zancenmu ga abu in muka nufaci halittarsa mu ce da shi kasance, sai ya kasance [Nahl, 40]). Sai Bishir ya ce “Ai duk wannan zancen dangantawa ce maras haqiqa. Misalinsa shine fadin larabawa sama ta ce wato ta yi ruwa, kamar kuma ka ce katanga ta ce wato ta karkace. Wato kamar fadin Allah (wata katanga tana son ta warware sai ya miqar da ita [Kahf 77]). Ka ga ai katanga ba ta da irada. Don haka, ma’anar (in muka nufaci halittarsa..) shine idan mun yi nufin kasantar da shi sai ya kasance”.
49. Bishir ba shi da wata hujja fiye da wannan. Kuma so yake ya ce  Allah ba ya magana.
50. Abu Ubaid, Alqasim Dan Sallam ya ce: “Kokarin da Bishir ya yi na kwatanta fadin Allah (in muka nufaci halittarsa.. ) da cewar mai magana (sama ta ce; watau ta yi ruwa) da kuma (bango ya ce; watau ya karkace) ba haka abin ya ke ba. Don kuwa in ka ce (sama ta ce) sai kai shiru ba za a gane me kake nufi ba, har sai ka ce (watau ta yi ruwa). Haka in ka ce (katanga ta yi nufin..) ba za a gane me kake nufi ba da lafazin (nufin) ba. Amma in ka ce (Allah ya ce…) wannan zance kowa zai iya fahimtar sa, don kuwa lafazin (ya ce) abin wadatuwa ne daga wani abu da zai cika ma’anarsa. Kamar yadda ka yi hujja da (katanga ta ce; watau ta karkace) don kuwa in ba haka ba to (katanga ta ce) ba shi zance ne maras ma’ana. Wanda duk ke fadin irin maganar nan ta Bishir to ba wani kafirci face ya zam yana kasa da shi. Wanda duk ya fadi irin wannan zance to yana yi wa Allah muguwar magana fiye da ta yahudu da nasara. Addininsa shine kore samuwar Allah”.
51. Aliyu Dan Madeeniy ya ce: “An ambaci Ibn Khalubah (wani bajahame a Basrah) Sai na ji Bishiru Dan Mufaddal yana cewa kafiri ne. An tambayi Wakee’u akan Muthannah Al-Anmatiy sai ya ce: kafiri ne. Abdullahi Dan Dawood ya ce: Da ina da hali da sai ba tuge harshen Muthannah Al-Anmatiy ta keyar sa”.
52. Sulaiman Dan Dawood Al-Hashimiy yana cewa: “Wanda duk ya ce Al-Qur’ani halitta ce, to ya kafirta. Kuma in da Al-Qur’ani halitta ne kamar yadda suke riyawa, me ya sa Fir’auna ya cancanci tabbata a gidan wuta saboda fadinsa cewa (Ni ne ubangijinku mafi daukaka [Nazi’at, 24]?)”.
53. Suna nufin wannan zancen na Fir’auna halitta ne? Kuma haka fadin Allah(Lallai ni ne Allah ba abin bauta face ni, don haka ka bauta mini[Taha, 14]?). Ma’anar maganar su ita ce: mai wannan zancen shi ma ya yi irin kurarin da Fir’auna ya yi. To a bisa wane dalili Fir’auna ya yi dacewa da azabar wuta bayan dukansu su biyun sun yi kirari ne iri daya a bisa riyawar su cewa duka biyun halitta ne? Sai aka bai wa Abu Ubaidin wannan labarin kuma sai abin ya burge shi”.
54. Ahmad Dan Muhamamad ya ce: “Ni na riga na gane cewa Jahamiyya kafirai ne”.
55. Fudayl Dan Iyad ya ce: “Idan bajahame ya ce maka shi bai yi imani da Allah wanda ke gushewa daga wuri ba, ka ce da shi ni kuwa na yi imani da Allah wanda yake aikata abin da ya so”.
56. Ibn Uyaynah ya ce: “Na ga Ibn Idrees a tsaye a kofar wata makarantar Allo sai na ce da shi baban Muhammad! Me ka ke a yi a nan? Sai ya ce mini ina sauraron zancen Ubangijina ne daga bakin wannan yaron”.
57. Yazeed Dan Haroon ya tsoratar akan jahamiyya sannan ya ce “Duk wanda ya fassara (الرحمن على العرش استوى) da sabanin abin da ke bijirowa a zuciyar mutum to bajahame ne”. Sannan ya ce: “Kuma Muhammadu Dan Hassan As-Shaibaniy bajahame ne”.
58. Daga Sadaqah ya ce na ji Sulaiman Attaimiy yana cewa: “In aka tambaye ni ina Allah yake? Sai na ce yana sama. In aka ce to a ina Al-Arshinsa yake kafin (halittar) sama? Sai na ce akan ruwa. In kuma aka ce to a ina yake kafin kan ruwan? Sai na ce ban sani ba”.
59. Abu Abdillahi ya ce: “Yana nufin saboda fadin Allah (Kuma ba zu iya kewaye wani abu na sanin sa ba sai abin da ya ga dama) watau sai abin da ya bayyana [Baqara, 255]”.
60. An ce da Muhammad Dan Yusuf: “Ka riski malamai, shin ka ji waninsu na cewa Al-Qur’ani halitta ne? Sai ya ce: Mai fadin wannan Magana shaidani ne. Bajahame ne kuma kafiri ne”.
61. Daga Muhammad Dan Qudamah ya ce: “Na ji Wakee’u yana cewa kar ku raina fadinsu (Al-Qur’ani halitta ne), don kuwa wannan magana tana daga cikin maganganu mafiya sharri. So suke su ce Allah ba shi da siffa”.
62. An ambaci Jahamiyya a gaban Alhassan Dan Musa sai ya ce: “Su waye su?” Sannan sai ya ba da labarin cewa “Wata rana an shigo da wani daga cikin jagororin Zanadiqah mai suna Shamgala fadar Sarkin Musulmi Mahadi sai ya tambaye shi ya ce: ka nuna min jama’arka, sai Shamgala ya ce: ai jama’ata sun fi karfin a nuna su da hannu. Mahadi ya ce: ka nuna min su. Sai ya ce: suna nan (a cikin ku musulmi); Bajahame idan yai nisa to za ka ji yana cewa ba Allah a sama. Baqadare idan yai nisa za ka ji yana cewa Alla biyu ne! Akwai na alheri, akwai na sharri. Nan take Mahadi ya sa aka kashe shi aka kuma gicciye gawarsa”.
63. Daga Yahya Dan Ayyub, ya ce: “Na ji Abu Nuaym Al-Balakhy yana cewa: “Akwai wani mutumin garin Marwa da ya kasance aboki ga Jahamu Dan Safwan, sa’annan daga baya suka bata, suka rabu baram-baram. Sai aka tambayi mutumin aka ce da shi: me ya sa ka bata da Jahamu? Sai mutumin ya amsa da cewa: Saboda (Jahamu) ya zo da abubuwa (marasa kyau) wadanda ba zan iya jure su ba. Sannan ya ce: wata rana na karanta wata aya a cikin Al-Qur’ani, sai Jahamu ya ce: gaskiya Muhammadu ya yi ban dariya! Nai shiru ban ce komai ba. Sannan wata rana na sake karanta Suratu Taha, da na zo kan fadin Allah (Allah mai rahama ya daidaita akan al’arshi[Taha, 5]), sai Jahamu ya ce: Na rantse da Allah da zai yiwu da na kankare wannan ayar daga cikin Al-Qur’ani! Nan ma na jure ban ce komai ba. Sa’annan (wata rana) sai (Jahamu) ya karanta Suratul Qasas, yayin da ya zo kan qissar Annabi Musa da ke cikin surar, sai ya ce: Wane irin shirme ne wannan? Wannan labarin an ambace shi a wani waje ba a kai qarshe ba! Sannan an zo an ambace shi anan ma ba a kai qarshe ba!. Sannan yai wurgi da Al-Qur’anin, kana ya shure shi da qafarsa, shine na tashi na rufe shi da duka”.
64. Abu Ja’afar ya ba ni labari cewa ya ji Yahya Dan Ayyub yana cewa: “Mun kasance, wata rana, a majalisin Marwan Dan Mu’awiya Al-Fazariy sai wani mutun yai masa tambaya akan hadisin ganin Allah, sai ya qi ya amsa masa. Sai mai tambayar ya ce: in dai ba ka amsa min ba to kai bajahame ne. Sai Marwan ya ce masa: Ni kake ce wa bajahame bayan Jahamu ya zauna kwana arba’in bai san Ubangijinsa ba?”
65. Abu Ja’afar ya ba ni labari, daga Haroon Dan Ma’aruf shi da Yahya Dan Ayyub suka ce: “Ibnul Mubarak ya ce: ko wadanne irin mutane sun san abin da suke bauta wa, amma banda Jahamawa”.
66. Daga Jareer, daga manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai za ku ga Allah Ubangijinku)
67. Yazeedu Dan Haroon ya ce: “Duk wanda ya qaryata wannan hadisi to ya yi baram-baram da Allah da manzonsa (SAW).
68. Abu Ja’afar ya ba ni labara, ya ce: Ahmad Dan Khalid ya ce: ya ji Yazeedu Dan Haroon ya ambaci Abubakar Al-Asam da Bishir Al-Mareesiy sannan sai ya ce: “Na rantse da Allah wadannan mutane guda biyu zindiqai ne, kafirai ne, sun bijire wa Allah, jininsu ya halasta.”
69. Abdurrahman Dan Mahadiy ya ce: “Wanda duk ya ce wai Allah bai yi magana da Musa ba to za a neme shi da ya tuba, in ya ki kuma a kashe shi”.
70. Maliku Dan Anas ya ce: “Al-Qur’ani maganar Allah ne”.
71. Yazeedu Dan Haroon ya ce: “Na rantse da Allah (Jahamiyyawa) zindiqai ne kuma mushrikai”.
72. An tambayi Abdullahi Dan Idris game da hukuncin sallah a bayan dan bidi’a. Sai ya ce: “Mutane ba su gushe ba suna sallah a bayan duk wanda ya iya sallah, matukar sun yarda da iyawarsa”. Sai a aka ce masa: “Allah shi gafarta malam! Har da Jahamiyyawa?”. Sai ya ce: “A’a! Banda Jahamiyyawa, su wadannan ba a bin su sallah, ba a auratayya da su kuma dole a neme su da su tuba”.
73. An tambayi Hafsu Dan Giyath game da Jahamiyyawa aka ce masa: “Abdullahi Dan Idris ya kafirta su”. Sai ya ce: “To ni dai ban san su ba”. Sai aka ce masa: “Wasu mutane ne masu cewa Al-Qur’ani Halitta ne” Sai ya ce: “Allah ya isa! Ka cuce ni! Ka fada min maganar da ta tayar min da hankali!” Sai aka ce masa: “Allah ya gafarta malam! Haka suke fadi”. Sai ya ce: “Bai halasta a yi auratayya da su ba. Haka nan bai halasta a karbi shaidar su ba”.
74. An tambayi Ibn Uyainah akan su [Jahamiyyawa], sai ya ba da fatwa kwatankwacin irin ta su Hafsu Dan Giyath. Sai na tafi wajen Wakee’u, sai na tarar da cewa ya san su sosai. Sai ya ce: “Ana kafirta su ta fuska kaza, ana kafirta su ta fuska kaza” har sai da ya kafirta su ta fuskoki da dama.
75. Sai Wakee’u ya ce: “Rafidawa sun fi Qadariyya sharri, su kuma duka biyun Haruriyya sun fi su sharri. Sannan Jahamawa kuwa, sun fi duka wadannan ‘yan bidi’a sharri a musulunci. Allah ya ce (Kuma Allah ya yi zance da Musa, zantawa). Amma su sun ce a’a, Allah bai zanta da Musa ba, sun kuma ce imani da zuciya ne kawai.
76. Alhassan Dan Rabee’u ya ce: “Wannan zance ne da su ne kawai suka kirkire shi”.
77. Baban Ja’afar ya ba mu labari ya ce: “Na ji Baban Munzir yana ba da labari daga wani wanda ya koyi karatu a wajen Mu’utamir Dan Sulaiman cewa: ya kasance yana ba da fatwa da cewa wanda duk ya ce Qur’ani halitta ne to dan bidi’a ne kuma mai fadin mummunar magana”.
78. Baban Abdullahi ya ce: “Mutumin shi ne Salamu Dan Ahwar; wanda shine ya kashe Jahamu Dan Safwan”.
79. Daga Jabiru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana gabatar da kan sa, a lokacin aikin hajji, yana cewa: wane ne zai kai ni cikin mutanensa…. Lallai Quraishawa sun hana ni isar da maganar Ubangijina.”
80. Anas Dan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da aka yi tafiyar dare da Manzon Allah (SAW) daga masallacin Ka’aba, ya ga Annabi Musa (AS) a sama ta bakwai (ya sami muqami ne) saboda maganar da Allah ya yi da shi.”
81. Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Allah ya ce kyauta ta magana ce, azaba ta magana ce, idan nai nufin yin wani abu cewa nake da shi kasance, sai ya kasance”.
82. Daga Abdullahi Dan Unays (Allah ya kara masa yarda) ya ce : “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: lallai Allah zai tashi bayinsa ranar Alqiyama sannan ya kira su da murya wacce na nesa zai ji kamar yadda na kusa zai ji. (Sai ya ce) Ni ne Allah mai mulkin komai. Ni ne mai hukunci da raba gardama. Bai dace wani daga cikin ‘yan aljanna ya shige ta ba alhali akwai wani haqqi na wani dan wuta a hannusa.”
83. Abu Hurayrah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Idan Allah ya hukunta wani al’amari a sama, sai mala’iku su dosa bubbuga fika-fikansu suna masu rankwafawa ga hukuncin Allah, karan fika-fikan kamar karan sarka akan falalon dutse. Idan aka yaye ma zukatansu (tsoron da ya kama su) sai su dinga cewa: me Allah ubangijinku ya fadi? Sai su ce ya fadi gaskia. Haka Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya fada da Ibn Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) da sauran malamai”.
84. Khabbabu Dan Arat (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “yi kokari ka kusanci Allah, (ka sani) ba za ka iya kusantar Allah ba da wani abu ba fiye da zancensa”.
85. Nayyar Dan Mukrim Al-Aslamiy (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lokacin da Suratur Rumi ta sauka Abubakar (Allah ya kara masa yarda)  ya fito yana cewa: maganar Ubangijina ce”.
86. Asma’u Yar Abubakar (Allah ya kara mata yarda) ya kasance duk sanda ta ji (ana karanta) Al-Qurani sai ta ce: “Zancen Ubangiji na”.
87. Abu Abdirrahman Assulami ya ce: “Darajar Al-Qur’an akan sauran maganganu, kamar darajar Allah ne akan bayinsa”.
88. Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na tambayi manzon Allah (SAW) na ce: ya manzon Allah! Waye farkon annabawa? Sai ya ce: Adam? Sai na ce: Shi ma annabi ne? Sai ya ce: Kwarai kuwa! Allah yana magana da shi”.
89. Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Yayin da Allah yai magana da Musa (AS) Allah ya kira shi ne daga sama, Allah ya kasance ne a sama”.
90. Musa Dan Mas’ud ya ba ni labari, ya ce Sufyan Dan Sa’id ya ba shi labara daga Abdurrahman Dan Abis ya ce: “Dalibai da dama daga makarantar Abdullahi Dan Mas’ud sun ba ni labarin cewa yana cewa: mafi gaskiyar zance shine maganar Allah”.
91. Abubakar Assidiq (Allah ya kara masa yarda) ya ambaci hadisin ceto daga manzon Allah (SAW) sai ya ce: “Nuhu (AS) ya ce: ku tafi wajen Ibrahim (AS), shine wanda Allah ya riqe shi babban masoyi. Sai su je wajen Ibrahim (AS) sai ya ce musu: ku je ga Musa (AS), shine wanda Allah yai magana da shi.”
92. Abu Hurayrah da shi da Ibn Umar (Allah ya kara musu yarda) sun ruwaito daga annabi (SAW) cewa: “Lallai Allah ya zabi Musa yai magana da shi kuma ya ba shi saqonninsa”.
93. Adiyyu Dan Hatim (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Allah zai yi magana da kowa daga cikinku, shi-da-shi ba tare da tafinta a tsakani ba. Sai mutum ya kalli damansa ba zai ga komai ba sai ayyukansa, ya sake duban hagunsa ba zai ga komai ba sai ayyukansa. Sai ya kalli gabansa ba zai ga komai ba sai wuta!. Ku guje wa wuta ko da da (sadakar) rabin dabino ne. (Ku guje wa wuta) ko da da (fadin) kalma mai dadi ne”.
94. Jabir Dan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce da ni: Ba na yi maka bushara da abin da mahaifinka ya samu (na falala) ba? Allah ya yi magana da mahaifinka ba tare da shamaki ba. Sai Allah ya ce masa: Ya kai bawana! Roke ni in ba ka duk abin da kake so. Sai ya ce: Ya Ubangijina! Ina so ka mai da ni duniya a sake kashe ni a wajen jihadi! Sai Allah ya ce: (Banda wannan) don na yi alqawarin in an mutu babu komawa duniya. Sai ya ce: To ka aika da wahayi don isar da labarin (falalar) da k aba (shahidai). Sai Allah ya saukar da fadinsa (Kar ka lissafa wadanda aka kashe a kan tafarkin Allah a cikin matattu. Don kuwa su rayayyu ne a wajen Allah (kuma) ana azurta su.” [Alu Imran, 169].
95. Baban Abdullahi ya ce: “Sunan Mahaifin Jabir Abdullahi Dan Amru Dan Hiram, ya yi shahada a yaqin Uhudu.
96. Jubair Dan Mud’im (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Daga Manzon Allah (SAW) ya ce: Lallai Allah ya daidaita a kan Al-Arshinsha saman sammansa. Kuma sammansa suna saman qassai ne kamar rufin daki”’
97. Ibn Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) yai bayani akan fadin Allah (Sa’annan ya daidaita akan Al-Arshi) [A’araf, 54] sai ya ce: “Al-Arshi yana saman ruwa, Allah yana saman Al-Arshi. Kuma ya san duk abin da kuke aikatawa”.
98. Qatadah yai bayani akan fadin Allah (Kuma shine Abin bauta a sama, abin bauta a kasa) [Zukhruf, 84] sai ya ce: “Ana bauta masa a sama, ana bauta masa a kasa’.
99. Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) yai bayani akan fadin Allah (Yana gudanar da al’amari daga sama zuwa kasa, sannan ya hauhawa zuwa gare shi a wata rana wacce take gwargwadon shekara dubu (1000) a bisa yadda kuke qirgawa) [Sajada, 5] sai ya ce: “na daga kwanakin shekara”.
100.  Kuma ya ce Allah ya ce: (Shin ko kun amince Allah wanda ke sama ya rufta muku da kasa sai ku gan ta tana motsi? Ko kuwa kun amince Allah wanda ke sama ya aiko muku da iska mai tsanani?) [Mulk, 17].
101. Imran Dan Husayn (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce da babana: “Allah guda nawa kake bautawa?” Sai ya ce: “Guda bakwai, shida a sama, daya a kasa”. Sai ya ce: “To wanne ne a cikinsu wanda kake kwadayin (rahamarsa) kake kuma tsoron (azabarsa)?”. Sai manzon Allah (SAW) ya ce masa: “Ka ga kuwa in da za ka musulunta da na koya maka wasu kalmomi guda biyu wadanda za su yi maka amfani”. Da ya musulunta sai ya ce: “Ya manzon Allah! Ka koya mini kalmomin da kai min alqawari”. Sai manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Allah ka kimsa min shiriyata kuma ka tsare ni daga sharrin kaina”.
102. Kabir Asgar ya ce: Sai dai malaman hadisi sun ce wannan hadisin bai inganta ba. Allah shi ne mafi sani.
103. Wasu malamai sun ce Jahamiyya sune Mushabbiha saboda sun kamanta Allah da gunki da kurma da wanda ba ya ji ba ya gani ba ya magana ba ya halitta.
104. Jahamiyya sun ce Allah ba ya magana kuma ba ya ganin kansa.
105. Jahamiyya sun ce: “Sunan ‘Allah’ halitta ne! Lazimin maganarsu shine idan ladani ya kira sallah su ce ya kira sunan halittar Allah tun da sun ce sunan Allah ma halitta ne.
106. Wata rana, wani musulmi ya yi rikici da wani bayahude, sai aka je gun shugabansu. Sai ya ce: musulmin ya rantse, sai ya rantse da Allah wanda ba sarki sai shi. Sai bayahuden ya ce: (ka ji shi) ya rantse da Mahalicci ba da abin halitta ba! Wannan maganar (لا إله إلا الله) akwai ta a Al-Qur’ani, amma kuma kai kana cewa (wai) Al-Qur’ani halitta ne. Anan aka kure mai musun gaskiya. Sai alqalin ya ce: ku tashi ku tafi, zan yi nazari akan shari’arku.
107. Daga Mu’awiya dan Ammar ya ce: “Na tambayi Ja’afar dan Muhammad game Al-Qur’ani sai ya ce: Al-Qur’ani ba halitta ba ne ba muka mahalicci ba ne”.
108. Baban Abdullahi ya ce: “Wadannan mutanen (wato Jahamiyya) sun yi hujja da ayoyi dabam dabam. Daga cikin ayoyin da suka kafa hujja da su akwai guda uku wadanda ke da rikitarwa mai tsanani”.
109. Aya ta farko ita ce fadin Allah (Madaukakin Sarki) (Kuma shi ya halicci komai sannan ya tsara shi matukar tsari) [Furqan, 2]. Sai (Jahamiyya) suka ce: in kun ce Al-Qur’an bai cikin “komai” kun kafirta. In kuma kun ce yana ciki to kun yarda halitta ne.
110. Aya ta biyu (ita ce) fadin Allah (Madaukakin Sarki) (Almasihu Isa dan Maryamu manzo ne na Allah, sannan kuma kalmar Allah ce da jefa ta ga Maryamu kuma ruhi ne daga gare shi) [Nisa’i, 171]. Sai suka ce: Ku (Ahlus-Sunnah) kuna fadin magana ne irin ta kirista cewa Almasihu kalmar Allah ce. Kuma kun san shi (Isa) halitta ne. Amma kuma kun ce: zancen Allah ba halitta ba ne. Kuma Isa yana daga cikin zance Allah.
111. Aya ta uku (it ace) fadin Allah (Madaukakin Sarki) (Ba wani ambato sabo da ke zo musu daga Ubangijinsu…) [Anbiya, 2]. Sai suka ce: Ku kuma kun ce ba sabo ba ne.
112.  Abu Ubaydah ya ce: “Dangane da fadin Allah (Kuma ya halicci komai..) haka maganar take. (Allah shi ne mahaliccin komai). Amma kuma Allah ya fadi a wani wajen ya ce: (Kadai maganar mu ga wani abu in mun nufaci [halittarsa] mu ce da shi kasance, sai ya kasance.) {Nahl, 40}. Ka ga ya ba da labarin cewa, farkon abin halittar da ya halitta ya halicce shi ne da maganarsa. Kuma wannan halitta ta farko tana cikin lissafin (abu) wanda Allah ya ce  game da shi (kuma ya halicci kowane abu…) Ka ga Allah ya ba labarin cewa maganarsa ta rigayi halittarsa”.
113.  Abu Ubaydah ya ce: “Dangane kuwa da kokarin Jahamiyyah na murde ma’anar hadin Allah (Kuma kalmarsa ce da ya wurga ta akan Maryam) {Suratun Nisa’i, 171}. Da a ce ayar tana bayar da ma’anar da kuke nufi ne to da cewa za a yi “Kuma kalmarsa ce ta ya wurga shi” ba “ya wurga ta” ba. Don kuwa lafazin “kalma” mace ce, amma lafazin “Isa” sunan namiji ne. Ayar tana nufin Allah ya halicci Isa ne da kalmar sa, ba wai shi Isa ne kalmar ba. Kai ba ka lura da cewa Allah ya ce ne: (Kuma kalmarsa ce da ya wurga ta akan Maryam da Ruhi daga gare shi ba) {Suratun Nisa’i, 171}. Wato Jibril (AS). A wata ayar kuma ya ce: (Sai muka aika mata ruhinmu sai ya zo mata a surar mutum madaidaiciya) {Maryam, 17}”.
114.  Kuma Allah ya ce: (Lallai misalin Isa a wajen Allah kamar misalin Adam ne. Allah ya halicce shi daga turbaya sannan ya ce da shi kasance sai ya kasance). {Alu Imran, 59}. Watau ya halicci Adam da Isa da kalmar (kasance). Babu wata sarkakiya a cikin wadannan ayoyi”.
115.  Amma dangane kuwa da fadin Allah (Ba wani ambato da zai musu sabo daga Allah…) Ambaton yana matsayin sabo ne a wajen Manzon Allah (SAW) da sahabban sa saboda Allah ya sanar da su abin da ba su sani ba”.
116. Baban Abdullahi ya ce: “Al-Qur’ani zancen Allah ne ba halitta ba ne. saboda fadin Allah (Lallai Allah Ubangijin ku da ya halicci sammai da kasa a cikin kwanaki shida, sannan ya daidaita akan Al-Arsh [Allah] yana lullube dare da wuni, yana nemansa ba kakkautawa. Kuma yana jujjuya rana da wata da taurari cikin umurninsa…) {A’araf, 54}”.
117. Baban Abdullahi ya ce: “Lallai halittu da nema da jujjuyawa duka suna gudana ne da umarninsa. Don haka ya cike maganar da cewa (Ku saurara! [Allah] shi ke da halitta da umarni. Allah Ubangijin talikai ya albarkantu.”
118.  Ibn Uyaynah ya ce: “Allah ya bambamce tsakanin halitta da umarni da cewar sa: Ku saurara! [Allah] shi ke da halitta da umarni. Watau halitta na samuwa ne da umarninsa. Kamar yadda ya ce a wani wajen: (Umarni na Allah ne, tun farko da kuma daga baya) {Rum, 4}. Da kuma fadin Allah Kadai umarninsa idan ya nufaci [halitta] wani abu sai ya ce da shi kasance, sai ya kasance) {Yasin, 82}.
119. Da kuma fadin sa cewa : (Kuma daga cikin ayoyinsa mikewar Sama da Kasa bisa umarninsa…) {Rum, 25}.
120.  An karbo daga Mujahid ya ce: “Na tambayi Ibn Abbas na ce da shi: mene ne Kaddara? Sai ya ce: ya kai Mujahid! Hala ba ka lura da fadin Allah ba ce: (Ku saurara! [Allah] shi ke da halitta da umarni)?”.
121.  An karbo daga Saidu Dan Jubair ya ce: daga Ibn Abbas ya ce: “Musulmai sun kasance suna fatan Rumawa su ci nasara akan Farisa saboda Rumawa suna bin addinin sama. Mushrikai kuma sun kasance suna son su ga Farisa sun yi galaba akan Rumawa saboda Farisa suna bautar gumaka. Sai musulmai suka ambata wannan labari ga Abubakar, shi kuma Abubakar sai ya ambata labarin ga Manzon Allah (SAW).  Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Lallai za a ci nasara akan su. Sai Abubakar ya fada musu abin da Manzon Allah (SAW) ya ce. Sai suka ce: To a sa lokaci; daga nan zuwa shekara biyar in an ci nasara akan Farisa za mu ba ka kaza da kaza, in kuwa an ci nasara akan Rumawa ka ba mu kaza da kaza. Bayan shekara biyar sai ba su ci nasara ba. Sai Abubakar ya ambata hakan ga Manzon Allah (SAW) sai ya ce da shi: me ya hana ka sanya musu kasa da shekara goma ba.
122. Saidu Dan Jubair ya ce: “Ana nan sai Rumawa suka ci nasara. Bayan an ci nasara akan su sai suka ci nasara akan Farisa. Allah ya ce: (Umarni na Allah ne, tun farko da kuma daga baya. Kuma a wannan ranar Muminai za su yi farin ciki da nasarar Allah) {Rum, 4}”.
123.  Baban Abdullahi ya ce: “Daga Huzaifatu Dan Yaman (Allah ya kara masa yarda) ya ce daga manzon Allah “Lallai Allah ya halicci duk wani abin da aka kera da wanda ya kera shi”. Baban Abdullahi ya ce: “sai wani daga cikin malaman ya karanta fadin Allah (Kuma Allah shi ya halicce ku da ku da ku da abin da ake aikatawa) {Saffat, 96}. Wato Allah yana bayyana cewa da ayyukan mutane da su mutanen duka halittunsa ne”.
124. Baban Abdullahi ya ce: “Daga Huzaifatu Dan Yaman (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Allah shi ya halicci igigar dabaibayi da wanda ke sana’ar hadata”.
125. Daga Ibn Abbas (Allah ya kara musu yarda) ya ce: “Da kwazo da lalaci dukansu suna cikin kaddara”.
126. Daga Dawus, ya ce: “Na riski mutane daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) suna cewa komai kaddara ne. Kumaa na ji Abdullahi Dan Umar yana cewa: Manzon Allah (SAW) ya ce: komai kaddara ne, har lalaci da kwazo”.
127. Laithu ya ce: “Daga Dawus daga Ibn Abbas (Allah ya kara musu yarda) ya ce: “Cewar Allah komai mun halicce shi da kaddara; har da lalaci da kwazo”.
128. Daga Abdullahi Dan Umar (Allah ya kara musu yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Komai an halicce shi ne da kaddara, har da lalaci da kwazo”.
129. Ibn Abbas ya ce: “Komai an halicce shi ne da kaddara, har da daura hannunka akan kumatunka”.
130. Baban Abdullahi, Muhammadu Dan Ismail ya ce: “Na ji Abdullahi Dan Said yana cewa ya ji Yahya Dan Said yana cewa: Ban gushe ba ina jin malamanmu suna cewa: Ayyukan bayi halittattu ne”.
131. Baban Abdullahi ya ce: “Motsin bayi da sautin muryarsu da ayyukansu da rubuce-rubucensu duka halittu ne. Amma shi wannan Al-Qura’ni da ake karanta, wanda ake rubuta shi a takarda kuma ake haddace shi ba halitta ba ne. Zancen Allah ne. Allah (STW) ya ce: (Shi ayoyi ne dalla-dalla a cikin kirazan wadanda aka bai wa ilmi)”.{Ankabut, 49}.
132. Ishaq Dan Ibrahim ya ce: “Ka ga su ababen amfanin (wato takarda da tawada da sauransu) ba wanda yake shakkar kasancewarsu halitta. Allah ya ce: (Kuma ina rantsuwa da littafi rubutacce, a cikin takarda wacce aka shimfida)” {Toor, 3}. Kuma ya ce: (Ai shi Al’Qur’ani littafi ne mai daraja. An ajiye shi a cikin wani allo tsararre) {Burooj, 22}. Haka Allah ya ambaci cewa ana rubuta shi kuma ana tsare shi a cewarsa: (Na rantse da abin da suke rubutawa) {Qalam, 1}”.
133. Daga Ummu Salama ta ce: “Na yi dawafi a daidai lokacin da Manzon Allah (SAW) yake sallah a kusa da dakin Ka’aba. Sai na ji shi yana karanta Suratu At-Toor)”
134. Baban Abdullahi ya ce: “Hakika Manzon Allah (SAW) ya bayyana zancen masu gode wa Allah a sallah da kuma adduarsu da sallarsu da risinawarsu ga Allah, yayin da shi kuma Allah Mabuwayin Sarki yake amsa musu”.
135. Baban Abdullahi ya ci gaba da cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “In kun so ku karanta: Bawa yana cewa (Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai). Sai Allah ya ce: (Bawana ya gode mini).
136. Daga Abus Sa’ib daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk sallar da ba a karanta fatiha a cikinta ba to wofi ci, ba ta cika ba”. Sai na ce da shi: “Ya Abu Huraira! To ya zan yi na karanta fatiha in ina bayan liman?” Sai ya ce: “Ka yi kokari ka karanta ta ko da a cikin zuciyarka ne, domin kuwa na ji Manzon Allah (SAW) ya ce: Allah (SWT)  ya ce: “Na raba sallah tsakanina da bawana, rabinta nawa ne, rabi kuma na bawana ne. Kuma bawana zai sami abin da ya roka a cikin sallah. Bawana yana cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai”. Sai Allah ya ce: “Bawana ya gode mini”. Idan bawa ya ce: “Allah mai rahama mai jin kai”. Sai Allah ya ce: “Bawana ya yabe ni”. Idan bawa ya ce: “Mamallakin ranar sakamako” Sai Allah ya ce: “Bawa na ya kururuta ni” Idan bawa ya ce: “Kai kadai muke bautawa, kuma gare ka kadai muke nema taimako”. Sai Allah ya ce: “Wannan tsakanina ne da bawana”. Idan bawa ya ce: “Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya”. Sai Allah ya ce: “Wannan ta bawana ne, kuma na ba shi abin da ya roke ni”.
137.  "Baban Abdullahi ya ce: “Amma ka gas hi kirgi da tawadar da ake rubuta Al-Qur’ani, to halitta ne. Kamar yadda in ka rubuta lafazin (ALLAHU) to shi Allh shi ne mahalicci. Amma rubutunka aikinka ne, kuma halitta ne. Domin kuwa komai wanda ya wannanci Allah halittarsa ce. Allah ya ce: (Kuma ya halicci komai sannan ya tsara shi matukar tsarawa) {Furqan, 2}.
138. Kuma Allah ya ce: (Kuma lallai shi Al-Qur’ani yana cikin Ummul-Kitab a wajenmu madaukaki ne kuma mai hikima) {Zukhruf, 4}.
139. Allah ya ce: (Lallai shi Al-Qur’ani littafi ne mai daraja, a cikin allo katangagge). {Burooj, 22}.
140. Daga Abu Huraira ya ce: “Maguzawan Makka ne suka zo suna jayayya da Manzon Allah (SAW) akan kaddara, a dalilin haka aka saukar da (Lallai mun halicci komai da kaddara) {Qamar, 49}.
141. Daga Amru Dan Shuaibu daga babansa daga kakansa, ya ce  fadin Allah (Lallai masu laifi suna cikin bata da kunar wuta) {Qamar, 47}ta sauka ne akan masu musun qaddara.
142. Haka ma aka ruwaito daga Abdullahi Dan Abbas da kuma Mu’azu Dan Anas (Allah ya kara musu yarda).
143. Daga Amru Dan Asim ya ce na ji Abu Huraira yana cewa “Abubakar ya roqi Manzon Allah (SAW) ya ce: Ya Manzon Allah! Ka koya min addu’a wacce zan dinga karantawa safe da maraice” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka dinga cewa:  Ya Allah Ubangiji! Ya Masanin boyayye da na sarari, ya Wanda ya halicci sammai da kasa. Ya Allah Ubangiji kuma Mamallakin komai. Ina shaida cewa babu abin bauta bisa gaskiya da cancanta bayanka. Ina neman tsarin ka daga sharrin kaina da sharrin shaidan da tarayyarsa”.
144. Daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Wanda duk ya ji kiran sallah sa’annan sai yai addu’a ya ce: (Ya Allah Ubangijin wannan cikakken kiran sallah da sallah wacce za a tada. Ina rokonka, ka ba Muhammadu Wasila da Fadilar da kai masa alqawari. Kuma ka tashe shi a matsayi abin yabawa. Lallai kai Allah ba ka saba alqawari) cetona ya tabbata gare shi.
145. Daga Anas Dan Malik shi da wasu cikin malaman farko game da ma’anar fadin Allah (Na rantse da Ubangijinka sai mun tambaye su game da abin da suke aikatawa) {Hijir, 92} ya ce “Za a tambaye su ne game da kalmar shahada”ز
146. Allah ya ce: (Wacan nan aljanna an ba ku ita ne saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa) {A’araf, 43}. Kuma ya ce: (Masu aiki su yi aiki akan misalin irin wannan aikin) {Saffat, 61}. Haka nan kuma ya ce: (Sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa) {Sajada, 17}.
147. [An ruwaito ta hanyoyi dabam-dabam] daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “an tambayi Manzon Allah (SAW) cewa wane aiki ne mafi falala? Sai ya amsa da cewa: Imani da Allah da kuma manzonsa. Sai aka ce: sai kuma wane? Sai ya ce: Sai kuma jihadi don tafarkin Allah. Sai aka ce: Sai kuma wane? Sai ya ce: Sai kuma aikin hajji karbabbe”.
148. [An ruwaito ta hanyoyi dabam-dabam] daga Abu Zarrin (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na tambayi Annabi (SAW) cewa: wane aiki ne ya fi falala? Sai ya ce “Imani da Allah da jihadi don Allah”.
149. [An ruwaito ta hanyoyi dabam-dabam] daga Aisha uwar muminai (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Wani mutum ya zo gun annabi (SAW) ya ce: wane aiki ne mafi falala? Sai ya ce masa: Imani da Allah da jihadi da kuma aikin hajji karbabbe”.
150. Daga Usman Dan Abu Hatmah daga kakarsa Asshafa’u (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Na ji an tambayi Manzon Allah (SAW) game da aiki mafi falala. Sai ya ce: Imani da Allah da jihadi da hajji karbabbe”.
151. Daga Ubadatu Dan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: wane aiki ne ya fi falala? Sai ya ce: Imani da Allah da gasgata manzonsa da kuma jihadi don hanyarsa”.
152. Daga Abdullahi Dan Habsh (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Daga Manzon Allah (SAW): Mafi falalar ayyuka shine imani wanda ba shakka a cikin shi”.
153. Daga Ubadatu Dan Samit (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: wane aiki ne ya fi falala? Sai ya ce: Imani da Allah da kuma gasgata littafinsa”.
154. Baban Abdullahi ya ce: “Ka ga Manzon Allah (SAW) ya lissafa imani da gasgatawa da jihadi a cikin ayyuka mafiya falala. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Wasu mutane za su bayyana, za ku raina [kyawun] sallarku in ga sallarsu, za ku raina [kyauwun] ayyukanku in kun kwatanta da aikinku in kun kwatanta da nasu. Suna karanta Al-Qur’ani amma ba ya wuce maqogoronsu. Suna ficewa daga addini kamar yadda kibiya ke ficewa daga kwari da baka.
155. Daga Qatadah game da fassarar fadin Allah (Kuma sun sanya masa wani sashe daga bayinsa){Zukhruf, 15}. Watau sun sanya masa tsara.
156. Hammadu Dan Zaid ya ce: “Wanda ya ce zancen bayi ba halitta ba ne ya kafirta”.
157. Baban Abdullahi ya ce: “Daga cikin dalilai akan cewa Allah yana magana yadda ya so a sanda ya so da kuma cewa zancen bayi yana samuwa ne daga hada haruffa da lankwasa murya da kwan-gaba-kwan-baya akwai hadisin Ummu Salma matar Manzon Allah (SAW) wanda Ya’ala Dan Mamlak ya tambaye ta game da karatun Manzon Allah (SAW) a cikin sallarsa. Sai ta ce: Ina ruwanku da sallarsa? Ya kasance yakan yi sallah sannan ya kwanta yai barci gwargwadon tsayin sallarsa, sannan ya tashi ya sake yin sallah gwargwadon tsayin barcinsa, sannan ya kwanta ya sake yin har zuwa asuba. Sannan ta siffanta karatunsa cewa harafi-harafi ya ke karatunsa”.
158. Daga Imran Dan Abdullahi ya ce: “Wani mutum ya yi mana sallah a masallacin Madina, sai ya yi karatu yana mai rerawa kamar waka, sai Qasim Dan Muhammad ya yi masa gyara, ya ce da shi: kai ba ka karanta fadin Allah ba ne: (Kuma shi littafi ne mabuwayi, barna ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko ta bayansa, shi saukakke ne daga Allah mai hikima kuma sha yabo){Fussilat, 42}”.
159. Daga Abdurrahman Dan Abu Sa’asa’ah, ya ce “mahaifinsa ya ce Abu Said Al-Khudriy ya ce masa: na ga kana son kiwo da zama a daji, in za ka yi sallah a daji ka kira sallah, kuma ka daga muryarka sosai, domin kuwa ba wani mutum ko aljani da zai ji sautin mai kiran sallah face ya yi masa shaida da imani a ranar alkiyama. Sannan Abu Said ya ce: Na ji wannan karatun ne a wajen manzon Allah (SAW)”.
160. Daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SWA) yana cewa: Ana gafarta wa mumini (in ya kira sallah) gwargwadon nisan sautin muryarsa”.
161. Daga Abdullahi Dan Zaid (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Yayin da Annabi (SAW) yai umarni da a hura kaho don sanar da lokacin Sallah sai nai mafarkin wani mutum ya zo yana yawo da kaho, sai na ce da shi: Bawan Allah kana sayar da kaho ne? Sai ya ce mini: Me za ka yi da shi? Sai na ce masa: Zan dinga amfani da shi ne wajen kiran Sallah. Sai ya ce: Shin ba na nuna maka abin da ya fi kahon alheri ba? Sai na ce: Kwarai kuwa”. (Sai ya koya masa kiran Sallah da Iqama). Sai ya ce: “Da gari ya waye sai na je gun Manzon Allah (SAW) na zayyana masa abin da na gani a mafarki” Sai ya ce min: “Wannan mafarkin alheri ne in Allah ya so. Tashi ka koya wa Bilal abin da ka gani don ya dinga kira mana Sallah saboda ya fi ka dadin murya”. Sai Umar Dan Khaddab (Allah ya kara masa yarda) ya jiyo daga cikin gidan sa ana laqqana wa Bilal kiran sallah din. Sai ya sheko a guje yana cewa: “Na rantse da Allah wanda ya aiko ka da gaskiya ni ma na yi mafarki irin wannan”. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allah”. 
162. Daga Ibrahim Dan Abdul-Azeez Dan Abdul-Malik Dan Abu-Mahzoorah ya ce: “Kakana ya ba ni labari cewa ya ji Abu Huraira yana cewa daga Manzon Allah (SAW) ya ce: Ka dinga jan sautin ka wajen fadin kalmar shahada da ke cikin kiran sallah. Kuma idan kun ji ladan yana kiran sallah ku dinga fadin irin abin da yake fadi. Da Umar Dan Abdul-Azeez ya ji Abu-Mahzoorah yana jan murya sai ya ce masa: “Kai Abu Mahzoorah! Ba ka jin tsoron kar mararka ta tsinke?” Ka kira mana sallah daidai-wa-daida ko kuma ka bar masallacinmu”.
163. Daga Urwah ya ce: “Aisha (Allah ya kara mata yarda) ta ambaci al’amarin Usman (Allah ya kara masa yarda) sai ta ce: Na yi burin ina ma a ce tuntuni na mutu an manta da ni [ban riski fitinar ba]. Na rantse da Allah! Ba wani abu na cin mutunci da nai fatan ya faru da Usman face sai da irinsa ya faru da ni. Wallahi da a ce na yi fatan a kashe shi to da ni ma an kashe ni. Ya kai UbaidulLahi Dan Adiyyu! Kar ka sake wani ya yaudare ka kana ji kana gani. Na rantse da Allah ban taba raina ayyukan sahabban Annabi (SAW) ba har sai da ‘yan tawayen da suka kashe Usman suka bullo da maganganunsu. Suka fada masa maganganun da ba zai iya fadin irinsu ba. Da karatun da ba zai iya irinsa ba. Da sallar da ba zai iya irinta ba. Amma da na tsaya na lura sai na gane cewa wallahi wadannan mutanen ko kusa ba su yi da sahabban Annabi (SAW) ba. Idan maganar mutum ta burge ka ka ce masa: (Ka ce ku yi aiki, Allah zai ga aikinku da manzonsa da muminai) Kar ka bari wani yai maka wasa da hankali.
164. Manzon Allah (SAW) ya ce da Jibrilu (AS) sa’adda ya tambaye shi game da imani: “Ka yi imani da Allah da Mala’ikunsa da Littafansa da Manzanninsa” Sai Jibrilu ya ce: “In nai haka na zama mumini?” Sai ya ce masa: “Kwarai kuwa”.  Sai ya ce: “To mene ne musulunci?” Sai Manzon Allah (SAW) ya amsa da cewa: “Ka shaida ba abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai Allah, kuma ka shaida cewa ni Manzon Allah ne”. Sai ya ce: “In nai haka na zama musulmi?” Sai ya ce: “Kwarai kuwa”… Sai ya ambaci hadisin zuwa karshensa.
165. Baban Abdullahi ya ce:  “Ka ga ya kira Imani da Musulunci da Shahada da Kyautayi da Sallah da abubuwan da ke cikinta na karatu da ruku’u da sujuda, ya kira dukan su da sunan aiyukan bawa. Kuma Allah ya ce: (Allah ya shaida babu sarki abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai Shi. Malaiku ma sun shaida hakanan mazowa ilmi). {Alu-Imran, 18}.
166. Daga Abu Zarrin shi da Abu Huraira (Allah ya kara musu yarda) suka ce: “Wani mutum ya zo ya ce wa Manzon Allah (SAW): Aminci ya tabbata a gare ka ya Muhammad. Sai Annabi (SAW) ya mayar masa da sallamar. Sai mutumin ya ce: Ya Muhammad mene ne imani? Sai ya ce masa: Imani shine gasgata Allah da Mala’iku da Littafi da Annabi da imani da kaddara dukanta. Sai ya ce: in na aikata haka nai imani? Sai Annabi (SAW) ya ce masa kwarai kuwa”.
167. Daga Umar Dan Khaddab (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana muna zaune a wajen Manzon Allah (SAW) sai wani mutum ya zo ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne Musulunci? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Shine mika al’amarinka ga Allah da tsai da Sallah da bayar da Zakka da Azumin Ramadan da Aikin Hajji…. Sai ya ce: Ka yi gaskiya”. Sai ya kawo hadisin zuwa karshensa.
168. Daga Anas Dan Malik (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana Manzon Allah (SAW) yana cikin sahabbansa sai wani mutum ya zo ya ratsa mutane har sai da ya zauna gaba gare shi ya sanya hannayensa akan gwuyawunsa, sannan ya ce: Mene ne Musulunci? Sai ya ce: Musulunci shine shaidawa ba abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai Allah da shaidawa cewa ni manzon Allah ne da tsayar da Sallah da bayar da Zakka da Azumin Ramadan da zuwa Aikin Hajji idan ka sami iko. Sai ya ce: in na aikata haka na zama mumini? Sai ya ce: Kwarai kuwa. Sai ya ce: Gaskiya ne. Sai sahabbai suka yi mamakinsa. Sai ya ce: To mene ne kyautayi? Sai ya ce: Ka tsoraci Allah kamar kana ganinsa, idan kai ba ka ganinsa ai shi yana ganinka. Sai ya ce: Yaushe za a tashi alkiyama? Sai ya ce: wanda ake tambaya bai fi wanda ke tambayar sani ba. Amma dai tana da alamomi. [Bayan dan lokaci] sai Manzon Allah (SAW) ya ce: a nemo min mutumin nan mai tambaya. Sai aka duba ba a gan shi ba. Sai ya ce musu:  Jibrilu ne ya zo [a siffar mutum] don ya koya muku addininku.
169. Daga Mu’awiyatu Dan Hakam (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce mini: wannan Sallah da muke yi bai dace a yi wani abu na zancen mutane a cikinta ba. Tasbeehi ne kawai da Kabbara da karatun Al-Qur’ani”.
170. Daga Tariq Al-Muharibiy (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ga Manzon Allah (SAW) yana shela, yana daga muryarsa yana cewa: Ya ku jama’a! Ku fadi kalmar Laa-ilaha-illal-Lahu za ku tsira”.
171. Kuma Annabi (SAW) ya ce da Ashajjun Abdu-Qais: “Kana da wasu halaye biyu wadanda Allah yake kauna; Hakuri da Kunya”. Sai ya ce: “Koyonsu na yi ko kuwa halitta ce?” Sai ya ce: “Dabi’a ce aka halicce ka a kai” Sai ya ce: “Na gode wa Allah da ya halicce ni akan dabi’ar halayen da yake so”.
172. Daga Abdurrahman Dan Abu-Bakratah daga Ashajjun Abdu-Qais cewa Manzon Allah (SAW) ya fada masa maganar da aka ambata kuma ya kara: sai na ce: “Dadaddiyar dabi’a ce ko sabuwa?” Sai ya ce: “Dadaddiya ce”.
173. Daga Amru Dan Shu’aibu daga babansa daga kakansa, ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan dayanku yai aure ko ya mallaki baiwa ko ya sayo abin hawa to ya dafa kan ta yai addua ya ce: Ya Allah ina rokonka ka ba ni alherinta da alherin da aka dabi’antar da ita akai. Ya Allah ka kiyashe ni daga sharrinta da sharrin da aka dabi’antar da ita akai”.
174. Baban Abdullahi ya ce: “Haka UbaidulLahi ya ruwaito shi daga Sufyan daga Ibn Ajlan daga Umar”.
175. Daga Abu Said (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Ya kai Ashajju! Hakika kana da wasu halaye da Allah yake so: natsuwa da bi a sannu. Sai ya ce: Ya Manzon Allah! Shin dabi’a ce aka halicce ni akai ko kuwa hali ne wanda na koya yau da gobe? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: A’ah. Dabi’a ce da aka halicce ka kai”.
176. Baban Abdullahi ya ce: “Al-Qur’ani zancen Allah ne kuma siffar Allah ne. Allah Mabuwayi yai magana da bayinsa. Hadisai da yawa sun bayyana cewa Al-Qur’ani zancen Allah ne kuma umarnin Allah ya rigayi halittar Allah kuma da urarninsa ya furta littafin.
177. Daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (SAW) ya ce: “Waye zai ba ni dama na zauna a cikin jama’arsa [don na isar da sakon Allah]? Hakika Quraishawa sun hana ni isar da zancen Ubangijina”.
178. Baban Abdullahi ya ce: “Ka ga Annabi (SAW) ya bayyana cewa isar da sakon shine aikinsa, amma sakon zancen Allah Ubangijinsa ne”.
179. [Baban Abdullahi ya ce]: “Ba wani [malami] cikin sahabbai Yyan Kaura ko Ansaru ko kuma wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa wanda ya fadi sabanin abin da muka fadi a nan. Wadannan mutanen (Wato Sahabbai da Tabi’ai) sune suka isar da Al-Qur’ani da Sunna bayan Manzon Allah (SAW)”.
180. Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Don ku zamo masu shaida akan mutane, shi kuma manzon ya kasance mai shaida akan ku [Baqara, 143]”.
181. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kune shaidun ah a [cikin] kasa”.
182. Daga Abu Said Al-Khudry (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: za a zo da Annabi Nuhu (AS) ranar alqiyama, sannan a tambaye shi: Shin ka isar da sakon Allah? Sai ya ce: kwarai kuwa ya Ubangiji, na isar. Sai a tambayi al’ummarsa: shin an isar muku da sakon Allah? Sai su ce: Mai gargadi bai zo mana ba! Sai a ce: [Ya kai Nuhu] su waye shaidunka? Sai ya ce: Muhammadu da al’ummarsa. Sai a zo da ku sai ku bayar da shaida [akan gaskiyar Nuhu (AS)]. Sa’annan sai Manzon Allah (SAW) ya karanta fadin Allah: (Kuma haka muka sanya ku al’umma tsaka-tsaki don ku kasance masu shaida akan mutane, shi kuma manzon ya zam mai shaida akanku [Baqara, 143]).
183. Baban Abdullahi ya ce: [Masu bayar da shaidar] sune mutanen da Manzon Allah (SAW) ya ce [game da su] “Wasu mutane cikin al’umma ta ba za su gushe ba suna bayyana gaskiya, wanda ya tabar da su ba zai iya cutar da su ba”.
184. Daga Mugiratu Dan Shu’ubah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Wasu jama’a cikin al’ummata ba zu gushe ba suna bayyane har al’amarin Allah ya zo suna bayyane.
185. Kuma an ruwaito kwatankwacin [wannan hadisi] daga Abu Huraira da Mu’awiya da Jabir da Salamatu Dan Nufail da Qurratu Dan Iyas (Allah ya kara musu yarda).
186. Baban Abdullahi ya ce: Babu sabani a tsakanin malamai [game da tabbatar da cewe Al-Qur’ani zancen Allah ne], har izuwa zamanin Maliku da [Sufyan] as-Sauriy da Hammad Dan Zaid da malaman birane. Sannan wadanda suka biyo bayansu, [kamar Sufyan] Dan Uyainah a cikin [malaman kasar] Hijaz da Yahya dan Saidu da Abdurrahman Dan Mahdiy a cikin malaman Hadisin [kasar] Basrah da Abdullahi Dan Idris da Hasfu Dan Giyath da Abubakar Dan Ayyash da tsararrakinsu da [kuma su] Ibnul Mubarak da mabiyansa da Yazeedu Dan Haroon cikin mutanen [garin] Wasid da kuma wadanda muka riska cikin malaman kasashen Makka da Madina da Kufah da Basrah da mutanen [kasar Sham] da Misra da malaman Hadisi a [kasashen] Khurasan. Irinsu Mumammad Dan Yusuf da mabiyansa da Abul Walid Hisham dan Abdulmalik da mabiyansa da Ismailu Dan Uwais tare da mutanen Madina, sai kuma Abu Mushirin cikin mutanen [kasar] Sham da kuma Nuaimu Dan Hammad tare da Misrawa da Ahmad Dan Hanbali tare da mutanen Basrah da Al-Humaidiy cikin Quraishawa da wadanda suka bi manzo cikin mutanen Makka. Da kuma Ishaq Dan Ibrahim da shi da Abu Ubaidin cikin malamai masana harshen Larabci.
187. Wadannan sune aka sani da ilimi a zamunnansu, gaba dayansu ba wanda ya saba wajen cewa Al-Qur’ani zancen Allah ne, in ban da wasu wadanda suka fandare suka kauce daga hanya madaidaiciya suka makance [daga ganin hanyar] alhalin suna ganinta.
188. Kuma lallai hujja ita ce Al-Qur’ani da Sunna. Allah ya ce: (Idan kun yi sabani akan wani abu, to ku maishe shi zuwa ga Allah da manzonsa [Nisa’i, 59]).
189. Daga Amru Dan Auf, ya ce “Manzon Allah (SAW) ya rubata cewa: duk abin da kuka yi sabani akan to ku mai da shi zuwa ga Allah da Manzonsa (SAW).
190. Kuma Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya aikata wani aiki ba tare da umarninmu ba to an mayar masa”.
191. Haka kuma Umar dan Khattab (Allah ya kara masa yarda) ya yi umarni da a mayar da duk wani abu da aka jahilta zuwa ga Al-Qur’ani da Sunnah.
192. Baban Abdullahi ya ce: “Duk wanda bai san Allah ba, bai kuma san cewa Al-Qur’ani zancen Allah ba ne, sai a mai da jahilcinsa ga littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (SAW).  Idan ya ki karbar gaskiya bayan an nuna masa ita to ya zama mai taurin kai.
193. Allah ya ce: (Kuma Allah ba zai halakar da mutane bayan ya shiryartar da su ba har sai ya bayyana musu abin da za su tsorata [Tauba, 115])
194. Kuma saboda fadin Allah: (Kuma wanda ke jayyaya da manzo bayan shiriya ta zo masa sannan yake bin sabanin tafarkin muminai to za mu jibintar masa abin da ya jibinta sannan mu sa shi a [wutar] Jahannama, kuma Jahannama ta munana [a matsayin] makoma[Nisa’i, 115]).
195. Abin da bangarori biyu dake kurarin bin tafarkin Ahmad [Dan Hanbali] suka kafa hujja da shi bai tabbata ba daga gare shi. Watakila kuma ba su fahimci maganganunsa ba.
196. Domin kuwa abin da ya tabbata daga Ahmad [Dan Hambali] da sauran malamai shine cewa Al-Qur’ani zancen Allah ne ba halitta ba ne. Duk abin da ya wannance shi kuma halitta ne.
197. Sannan kuma malaman suna kyamar shisshigi da yin bincike akan abubuwa masu sarkakiya. Kamar yadda suka guje wa biye wa masu kutse da jayayya cikin abin da ilmin [annabta] bai zo da shi ba.
198. Daga Amru Dan Shu’aibu daga babansa daga kakansa ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ji wasu mutane suna jayayya sai ya ce: Irin wannan [jayayyar] ce ta halakar da wadanda suka rigaye ku; sun kasance suna gwara sashen littafin Allah akan wani sashen. [Ku sani cewa] littafin Allah ya sauka ne yana mai gasgata bangarorin junansa. Ku daina gwara sashensa akan wani sashe. Ku yi magana akan abin da kusa sani a cikin sa, abin da ba ku sani ba ku fawwala shi ga masaninsa”.
199. Baban Abdullahi ya ce: “Duk wanda wani abu ya shige masa duhu, abin da ya fi dacewa da shi shine ya fawwala shi izuwa ga wanda ya san shi. Kamar yadda Abdullahi Dan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya fadi cewa: Ku fawwala abin da ya shige muku duhu izuwa ga masaninsa. Kar ku dinga kutsawa cikin sarkakiyar abubuwa masu rikici”.
200. Daga Aisha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Manzo Allah (SAW) ya karanta fadin Allah: (Shine [Ubangiji] wanda ya saukar maka da littafi, a cikinsa akwai ayoyi masu bayani dalla-dalla, sune mafi yawa a littafin. Da kuma wasu [ayoyin] masu sarkakiya. Wadanda ke da karkata a zuciyoyinsu suna biye wa abin da ke da sarkakiya don neman ta-da-zaune-tsaye da kuma nufin canza fassara. Kuma ba wanda ya san [hakikanin] fassararsa sai Allah. Da kuma wadanda suka kware a ilimi suna cewa: mun yi imani da shi, dukkan shi daga Ubangijinmu ne, ba masu wa’azantuwa sai ma’abota hankali [Alu Imran, 7])”.
201. Aisha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Sannan Annabi (SAW) ya ce: idan kuka ga masu bibiyar abin da ke da sarkakiya a Al-Qur’ani to ku kiyaye su, sune wadanda Allah yake nufi”.
202. Ibn Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wanda ya san wani abu na ilmi to yai magana akan ilmi, wanda kuwa bai sani ba to ya ce: Allah shine mafi sani. Lallai fadin Allah (SWT) shine mafi sani na nuni izuwa ga ilmin mai fadin hakan. Domin kuwa Allah (SWT) ya ce da Manzonsa (SAW): (ka ce ba na tambayarku wani lada akan sa, kuma ni ba na daga cikin masu daukar-kano-ba-gammo [Saad, 86])”.
203. Daga Masrooq, ya ce: “Na je gun Ibn Mas’ud sai ya fadi magana irin wacce aka ambata [a sama] har ma ya kafa hujja da fadin Manzon Allah (SAW) cewa: Ya Allah ka gafarta wa mutane na, lallai ba su sani ba ne. Idan ka ga kwadayi yai yawa, kuma an biye wa son zuciya, sannan duniya ta shagaltar da mutane, hakanan kowa ra’ayinsa ne ke burge shi, to ka yi ta kanka ka fita batun mutane”.
204.  Daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Kalmomi guda biyu, wadanda Allah mai Rahama ya ke so, masu sauki ne akan harshe, masu nauyi ne akan ma’auni: tsarki ya tabbata ga Allah da kuma godiyarsa, tsarki ya tabbata ga Allah Mai Girma”.
205. Daga Abdullahi Dan Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wata rana wasu mutane uku, biyu Quraishawa dayan kuma Thaqafiy ne, ko kuma biyu Thaqafawa dayan kuma Baquraishe ne. Mutanen masu katon tumbi ne amma kuma masu karancin fahimta. Sai dayan su ya ce: Wai kuna ganin Allah yana jin abin da muke cewa kuwa? Sai dayan ya ce: In mun bayyana yana ji, amma in mun asirta ba ya ji. Sai na ukun ya ce: In dai yana iya jin mu in mun bayyana, to kuwa yana jin mu ko mun asirta. Sai Allah ya saukar da aya (Kuma ba ku kasance kuna boye [sabon da kuke yi ba daga gabobinku] don kar kunnuwanku da idanuwanku da al’aurarku su yi muku sheda…[Fussilat, 22])”.
206.  Daga Yahya Dan Atiq daga Ibn Seereen ya ce: “Mutane sun kasance suna yawan magana akan [mu] ‘yan kasuwa, sai ka ji suna cewa: muna mamakin su wane! Ya suke yi a kasuwanci? Sai Yahya ya ce: [Ai kamata ya yi] ya dinga yin gaskiya da kaza da kaza” Muhammadu [Dan Seereen] ya ce: sai da Yahya [Dan Atiq] ya shiga [harkar] kasuwa, sai na ji shi yana fadin: Ya dan uwana! Wallahi ba wani abu face sai da ya shige min duhu. Sai na bai wa Humaid Dan Abdurrahman labarinsa, sannan na ce masa, yanzun kenan da yai hankali.”
207. Daga Huzaifa (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani lokaci zai zo ya riski mutane, ba abin da zai samu karbuwa a lokacin sai abubuwan da aka hana mutane”.
208. Baban Abdullahi ya ce: “Ma’anar fadin Allah (Kuma ka kau da kai daga jahilai [An’am, 159]) sune wadanda ke rarrabuwa kamar rabuwar ‘yan bidia. An ambato daga Dawoos daga Abu Huraira ya ce: (Suna cikin wannan al’umma)”.
209. Daga Sha’abiy, yai bayani akan hukuncin sayar da mus-hafi cewa ai ba littafin Allah ake sayarwa ba. Mutum yana sayar da aikin sa ne da yayi [na kwafewa].
210. Daga Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “ka sayi mus-hafi amma kar ka sayar da shi”.
211. Bukairu Dan Mismar ya ce: “Ziyadu, bararren bawan Sa’ad ya ba ni labarin cewa ya tambayi Ibn Abbas akan hukuncin sayar da mus-hafi sai ya ce: Ni ba na ganin dacewar a mai da sayar da Al-Qur’ani sana’a, amma ba laifi ka sayar da wanda kai aikin kwafewa da hannunka”.
212. Daga Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Mun kasance ba ma ganin laifin mutum ya sayar da mus-hafi don ya sayo wanda ya fi wancan nagarta. Haka nan ba laifi yin musayar mus-hafi da mus-hafi, daga nan ne aka yi rangwame a kan sayen mus-hafi”.
213. Daga Ubaidullahi Dan Suleiman ya ce: “Na tambayi Saidu Dan Musayyib game da hukuncin sana’ar kwafe mus-hafi, sai ya ce: babu laifi, wani yaron gidan Ibn Abbas ya kasance yana rubutawa ya karbi 100”.
FASSARAR LITTAFIN (HALITTA AYYUKAN BAYI) NA AL-IMAMUL BUKHARIY

Posting No. 57

214. Daga Abuz Zubair, ya ce “na ji Jabir Dan Abdullahi (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) yana cewa: Na fi son in sayi Al-Qur’ani fiye da in sayar da shi”.
215. Daga Ibn Abbas (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Masu rubuta Mus’hafi suna cin kudin aikin da suka yi ne”.

216. An ambata daga Aliyu (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Wani zamani zai riski mutane, wanda ba abin da zai saura a addini sai sunansa, ba abin da zai saura a Al-Qur’ani sai rubutunsa”.

217. Annabi (SAW) ya ce: “Ku kawata Al-Qur’ani da muryoyinku”.

218. Daga Abu Hurairah (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) ya ce: ba abin da Allah yai wa wani annabi izini kamar yadda yai wa annabi izinin rera Al-Qur’ani”.

219. Baban Abdullahi ya ce: “Kuma Manzon Allah (SAW) ya saurari qira’ar Abu Musa [Al-Ash’ariy] sannan ya ce: an ba Abu Musa [muryar] serewa irin ta [Annabi] Dawud”.
220. Daga Bara’u ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ji qira’ar Abu Musa sai ya ce: wannan murya ta yi kama da muryar Annabi Dawud”.
221. Daga Shuraih, ya ce: “Abu Hani’i Dan Yazeed (Allah ya kara masa yarda) ya ce: na tambayi Annabi (SAW) cewa ya fada min abin da zan aikata wanda zai shigar da ni aljanna, sai ya ce min: ka dinga fadin magana mai kyau, kuma ka dinga ciyar da abinci”.
222. Daga Amru Dan Harith (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa wanda ke so ya karanta Al-Qur’ani kamar yadda aka saukar da shi to ya karanta shi da karatun Ibn Ummi Abdin”.
223. Maisara, bararren bawan Fadalah ya ce daga Fadalah Dan Ubaid (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: sauraron Allah ga mutumin da ke da dadin murya wajen karatun Al-Qur’ani ya fi tsanani fiye da [sauraron] ma’abocin sarewa ga sarewarsa”.
224. Daga Abu Musa Al-Ash’ariy (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: lallai ni ina gane ayarin Ash’ariyyawa in sun shigo [Madina] da dare. Haka kuma ina gane ina ne masaukinsu da dare a [Madina] saboda dadin muryar [karatun] su, ko da ban san masaukinsu da rana ba. Kuma a cikinsu akwai wani mai hikima wanda in ya gamu da mahaya sai ya ce musu: lallai mutane na umurtarku da ku jira su”.
225. Daga Abdurrahman Dan Ausajah daga Bara’u (Allah ya kara masa yarda) daga Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku dinga qawata Al-Qur’ani da muryoyinku”. Abdurrahman ya ce: “Sai na manta karatun, sai da Dahhaku Dan Muzahim ya tuna mini.
226. Baban Abdullahi ya ce: “Daukacin wadannan hadisai sun tabbata daga mazowa ilimi. Kuma ba shakku akan cewa muryar ‘Alu Dawud’ halitta ce. Saboda fadin Allah (Kuma ya halicci komai) da kuma fadinsa (Kar ku sanya wa Allah kishiyoyi alhalin kuna sane).
227. Daga Adiyyu Dan Thabit ya ce: “Na ji Bara’u yana cewa na ji Manzon Allah yana karanta (Watteeni Wazzaitun) a sallar Isha’i. Ban taba jin wani wanda ya kai shi dadin murya ba”.
228. Daga Naufal Dan Iyas Al-Huzaliy ya ce: “Mun kasance a zamanin halifancin Umar muna sallar dare da azumi a masallaci, sai mutane suka dosa rabuwa kungiya-kungiya. Kuma mutane sun kasance suna karkata izuwa ga wanda ya fi dadin murya a cikinsu. Sai Umar ya ce: Na lura cewa mutane sun mayar da Al-Qur’ani waka. Na rantse da Allah in na sami hali sai na hana su. Bayan kwana uku sai ya umarci Ubayyu [Dan Ka’ab] yai musu sallah”.
229. Daga Alqamah ya ce: “Abdullahi [Dan Mas’ud] ya ce  da ni: karanta min Al-Qur’ani, dama Alqamah ya kasance mutunn ne mai dadin murya. Sai ya karanta, sai Abdullahi Dan Mas’ud ya ce  masa: rera min karatun, na ba ka fansar uwa da ubana”.
230. Allah ya ce: (Idan ana karanta Al-Qur’ani ku yi shiru kuma ku saurara [A’araf, 204]).
231. Allah ya ce: (Kuma ka karanta musu abin da aka yi maka wahayi na daga littafin Ubangijinka [Fatir, 29]).
232. Kuma Allah ya ce: (Wadanda ke tilawar littafin Allah [Kahfi, 27]).
233. Kuma ba ka kasance gabanin sa kana karatun wani littafi ba, kuma ba ka rubuta shi da hannunka [Ankabut, 48]).
234. Kuma Allah ya ce: (Suna karanta shi, karantawa ta gaskiya [Baqara, 121])
235. Kuma Allah ya ce: (Kuma ku dinga ambaton abin da ake karantawa a gidajenku na daga ayoyin Allah da kuma hikima [Ahzab, 24]).
236. Kuma Allah ya ce: (Suna karanta ayoyin Allah cikin dare [Alu Imran, 113]).
237. Kuma Allah ya ce: (Lallai wannan Al-Qur’ani yana shiryatarwa zuwa ga abu mafi zama daidai [Isra’i, 9]).
238. Baban Abdullahi (Allah ya ji kansa) ya ce: “Sai ya bayyana cewa karatun daga Manzon Allah ne (SAW) shi da sahabbansa (Allah ya kara musu yarda). Amma wahayin daga Allah ne. Kamar yadda Aisha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Ban taba tsammanin Allah zai aiko da wahayi abin karantawa ba akan sha’anina”.
239. Sai [Aisha] (Allah ya kara mata yarda) ta bayyana cewa saukarwar daga Allah ne, ita kuma tilawar daga mutane ne.
240. Daga Urwatu Dan Zubair da Saidu Dan Musayyib da Alqamah Dan Waqqas da UbaidulLahi Dan Abdullahi dukkansu daga Aisha (Allah ya kara mata yarda) yayin da masu yada labarin qazafin da aka yi mata suka yada shi, sai ta ce: “Sai na kwanta akan shimfida ta, ina mai yaqinin cewa qazafi ne aka yi mini, kuma na tabbatar Allah zai bayyana gaskiya ta. Amma na rantse da Allah ban taba tsammanin Allah (SWT) zai saukar da wahayi wanda za a dinga tilawarsa ba akan al’amarina. A ganina, matsayina bai kai a ce Allah (SWT) ya yi magana akan al’amarina da wahayi ba. Sannan sai Allah ya saukar da fadinsa (Lallai wadanda suka zo da labarin karya wasu tsiraru ne daga cikinku…) Ayoyi goma”.
241. Baban Abdullahi ya ce: “Allah ya ce: (Da a ce mutane da aljanu za su yi taron dangi don su samar da irin wannan Al-Qur’ani ba za su iya samar da irinsa ba, ko da kuwa wasunsu na taimaka wa wasu [Isra’i, 88]).
242. Don kuwa shi [Al-Qur’ani] zancen Allah ne wanda mutane da mala’iku ke furta shi”.
243. Daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan Allah ya kaunaci bawansa, sai ya kirawo [Mala’ika] Jibrilu [ya ce masa]: ina son wane. Sai Jibrilu ya bayyana wa [mala’ikun] dake dauke da Al-Arshi. Sai su ma su [mala’ikun] su kaunace shi. Sai mala’ikun sama ta bakwai su jiyo sautin mala’ikun da ke dauke da Al-Arshi… Sai ya ambaci hadisin”.
244. Allah ya ce: (Kadai mun sauqaqa shi da harshenka [Maryam, 91]).
245. Allah ya ce: (Hakika mun saukaka Al-Qur’ani domin Ambato[n Allah] [Qamar, 71]).
246. Daga Imran Dan Hussain (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Kowa ana saukake masa abin da aka halicce shi domin sa”.
247. Daga Imran (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na tambayi Annabi (SAW) cewa mene ne amfanin aikin masu aiki? Sai ya ce: Ai kowane mutum an saukake masa abin da aka halicce shi domin sa”.
248. Daga Jabir (Allah ya kara masa yarda) daga Manzon Allah (SAW): “Kowa ana saukake masa aikinsa”.
249. Abdullahi Dan Umar (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Daga Manzon Allah (SAW): kowa ana saukaka masa qaddararsa”.
250. Daga Abdullahi Dan Umar (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Babana ya ce: daga Manzon Allah (SAW) ya ce: kowane mutum an saukake masa abin da aka halicce shi domin so ".
251. Baban Abdullahi ya ce: “Annabi (SAW) ya bayyana cewa ambaton Allah shine aikin”.
252. Daga Mu’azu Dan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Lallai kalma ta karshe da na yi bankwana da Manzon Allah (SAW) akan ta ita ce: na tambaye shi cewa ya Manzon Allah! Wane aiki ne ya fi soyuwa ga Allah (SWT) ko ya fi falala? Sai ya ce: Ka mutu alhalin harshenka yana danye akan ambaton Allah”.
253. Daga Abdullahi Dan Mugaffal (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Na ga Manzon Allah (SAW) yana kan rakumarsa, tana tafiya da shi, shi kuma yana karanta Suratul Fathi, ko kuma yana karanta wasu ayoyi a cikin Suratul Fathi karatu mai sauki, yana ta maimata haruffan karatun”.
254. Daga Mu’awiyatu Dan Qurrah daga Abdullahi Dan Mugaffal (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Annabi (SAW) ya karanta Suratul Fathi ranar da aka bude Makka sai yai ta maimata karatun” Sai Mu’awiyatu Dan Qurrah ya ce: “Da na ga dama da sai na kwatanta muku irin karatun Annabi (SAW).
255. Baban Abdullahi ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa wane ne mafi kyawun karatu a cikin mutane? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Shine wanda idan ka saurare shi za ka ga alamar cewa yana tsoron Allah (SWT).
256. Kuma ana ambata daga Sa’idu (Allah ya kara masa yarda) daga Manzon Allah (SAW) cewa: mafi kyawun ambaton Allah shine wanda aka yi a boye [domin Allah] ya ce: (Ku kirayi Ubangijinku kuna masu rankwafa wa gare shi kuma a boye [A’araf, 55]), kuma [Allah] ya ce (Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin ranka kana mai rankwafawa a gare shi, kuma a boye da kuma abin da ke kasa da bayyana zance [A’araf,205].
257. Mu’azu Dan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya ji wani makaranci yana daga muryarsa sanda yake karatu sai ya ce masa: “Lallai murya mafi zamantowa abin kyama ita ce muryar jaki”.
258. Daga Abu Usman ya ce: “Ban taba jin wani goge ko sarewa ko ganga da zakinta ya kai dadin muryar Abu Musa ba, sai dai ko wane, wanda ya kasance yana yi mana sallah sai mu yi ta fatan ina ma ya karanta Suratul Baqara saboda dadin muryarsa”.
259. Daga Mu’azu Dan Jabal (Allah ya kara masa yarda) ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: “Ya Manzon Allah! Shin za a kama mu da duk abin da muke fadi?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce masa: “Shin akwai wani abu da zai sa a kikkifa fuskokin mutane a cikin gidan wuta fiye da abubuwan da harsunansu suke fadi?”.
260. Baban Abdullahi ya ce: “Ka ga Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa muryoyin halittu da karatun su da darasinsu da karantarwarsu sun bambamta. Akai mai dadi, akwai mai zaki, akwai mai lahani, akwai madaukaki, akwai na kasa, akwai mai natsuwa akwai kwararre akwai mai jan madda. Allah ya ce: (Kuma muryoyi suka natsu ga Allah Mai Rahama, ba ka jin komai sai rada [Taha, 108])”.
261. Daga Aisha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: Gwani a wajen tilawar Al-Qur’ani yana tare da jakadu, zababbun malaiku masu daraja. Wanda kuwa ke karanta shi da kyar yana da lada biyu”.
262. Daga Qatada ya ce: “Na tambayi Anas [Dan Malik] (Allah a kara masa yarda) cewa ya yanayin karatun Manzon Allah (SAW)? Sai ya ce: ya kasance yana jan maddoji [a karatunsa]”
263. Daga Qatada ya ce: “An tambayi Anas [Dan Malik] (Allah a kara masa yarda) cewa: yaya Manzon Allah (SAW) ya ke karatunsa? Sai Anas ya ce: ya kasance yana jan maddojin karatun. Sannan sai Anas ya ce: yana karanta (bismillahi) sai ya ja, ya karanta (arrahmani) sai ya ja, ya karanta (arrahimi) sai ya ja”.
264. Daga Qudba Dan Malik (Allah ya kara masa yarda) daga Manzon Allah (SAW) cewa ya karanta fadin Allah (Kuma da [bishiyoyin] dabino manya-manya wadanda suke da huda da yabanya mai yawa [Qaf, 10]) yana ta jan muryarsa da karatun.
265. Baban Abdullahi ya ce: “Amma shi abin da ake karantawar, zancen Allah ne wanda ba wani abu irinsa kuma shi mai ji ne kuma mai gani. Allah ya ce: (Wannan littafinmu ne yana muku magana da gaskiya [Jathiyah, 29]).
266. Daga Abdullahi Dan Amru Dan Ass (Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: za a mai da Al-Qur’ani [kamar] wani mutum ranar alkiyama sai ya zo ya ceci ma’abocinsa”.
267. Baban Abdullahi ya ce: Shine kasabinsa da aikinsa.
268. Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Wanda ya aikata alheri daidai da komayyar zarra zai gan shi, wanda kuma ya aikata daidai da komayyar zarra na sharri zai gan shi [Zilzila, 8]).
269. Daga Sa’asa’ah; Baffan Farasdaq, ya ce: “Na je gun Manzon Allah (SAW) sai na ji shi yana karanta [fadin Allah] (Wanda ya aikata alheri daidai da komayyar zarra zai gan shi, wanda kuma ya aikata daidai da komayyar zarra na sharri zai gan shi [Zilzila, 8]). Sai na ce: [Wannan] ya ishe ni. Na san ina alheri yake, ina sharri yake.
270. Ibn Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Mu [sahabbai] in mun fada muku magana, to za mu fada muku abin da ke gasgata ta a cikin Al-Qur’ani. Kuma hakika, daga cikin abin da ke shiga cikin haka akwai karatun Al-Qur’anin.
271. Hakika Allah ya bayyana wa halittunsa cewa (Shine wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don ya jarabta [su ya ga] waye a cikinku yafi kyawawan ayyuka [Mulk, 2]).
272. Sai Allah ya bayyana wa halittunsa cewa aiki na cikin rayuwa sannan kuma sai ya ce: (Kuma ko ku boye zancen ku ko ku bayyana, lallai shi masani ne an abin da ke cikin qiraza. Ashe wanda yai halitta kuma ya kasance mai tausasawa kuma mai bayar da labara ba zai sani ba [Mulk, 14]).
273. Tare da cewa Jahamiyyah da Masu barnatar da siffofin Allah suna jayayya da malamai ne akan zancen Allah. [Suna cewa] Allah ba ya magana, kuma in ma har yana yi to maganarsa halitta ce. Sai suka ce Al-Qur’anin da ake karantawa da ilimin Allah halitta ne. Ba su bambamce ba tsakanin tilawar bayin [Allah] da kuma shi abin karatun ba. Kuma hakika Abubakar (Allah ya kara masa yarda) ya daga muryar sa da cewa (Shin za ku kashe mutum ne don kawai ya ce: Allah ne ubangiji na [Gafir, 28]).


No comments:

Post a Comment