Wednesday, May 8, 2019

Hukuncin daukan azumi a wani gari da ajiyewa a garinda lissafin watansu ya bambanta

TAMBAYA: menene hukuncin Wanda yadauki azumi a kasarsa ,sai kuma yaje wat kasar ya Tatar watansu ya bambanta Dana kasarsa ?misali kamar masu zuwa saudiyyah aikin umrah wani lokaci su Tatar da Satan saudiyyah yana ashirin da takwas, alhali NASA ya cika ko kuma nasu ya cika , NASA kuma na ashirin da takwas. Yaya zai yi?

AMSA:zai bi nasu lissafin ne koda azuminsa zai wuce talatin.idan kuma nasa bai cika ba ,alhali su lissafinsu ya cika ,zai ajiye azumin domin yayi sallah tare dasu daga baya sai ya rama abinda b
ai riska ba .dalili na cikin hadisin da aka karbo daga Nana Aishah (RA)tace manzon Allah (SAW)yace:
        Bude bakinku (ajiye azumi) shine ranar da mutane ke bude baki (ajiye azuminsu),layyarku itace ranar da mutane suke layya.
   (Sunan Abu dawud (2324),sunan ibn majah(1660)kuma sheikh Muhammad nasiruddeen albani ya ingantashi acikin irwa al-ghalil(905)
Hadisin ya nuna cewa jama'ar da ya Tatar  a garin ,idinsu shine idinsa , kuma shan ruwansu shine shan ruwansa ,haka kuma idan Anne acikin hajji za a bisu a kowane irin aiki visa lissafinsu
      (Duba fatawa al-lajnatu da imah lil buhuthil ilmiyyah wal ifta.10/123-124

Daga Lotta finds tawny in azumin Ramadan na shaikh abdulwahab abdullah

Domin samun cikakkun fatawoyin musulunci sai a nememu a shafinmu na zinariyah.blogspot.com


No comments:

Post a Comment