Saturday, May 4, 2019

ALBISHIR DIN ANNABI (SAW)AKAN RAMADAN


*TAMBAYA:Wane irin albishir manzon Allah (saw) yake yiwa al'ummarsa kafin Satan Ramadan ya kama?
AMSA:Manzon Allah (saw) ya kasance yana yiwa al'ummarsa bushara da zuwan Ramadan.yana cewa:
Idan watan Ramadan ya shigo ana bude kofofin rahama da kofofin aljannah,kuma ana rufe kofofin jahannama,kuma ana daure shaidanu.
       ( sahihul bukhari (1898,1899),da Muslim (2/1079)
Haka kuma an ruwaito daga anas ibn malik (RA) yace: watan Ramadan ya shigo sai manzon Allah (saw) yace :
  Lallai wannan wata na Ramadan hakika ya halarto muku , acikinsa akwai wani dare Wanda yafi  dubu alheri.duk Wanda aka haramta  masa ( samun alherin dake cikinsa ) hakika an haramta mass alkhairi dukansa . kuma babu Wanda ake haramta was alherinsa sai Wanda bashida rabo.
      (Sunan ibn majah (1644),kuma sheikh al bani a cikin sahih al targhib yace hadisin hasan ne
  
Daga
Littafin fatawoyin azumin Ramadan .na shaikh abdulwahab abdullah
Domin samun cikakkun fatawoyi akan mas'alolin addini sai a neme mu a shafin mu na ZINARIYAH.blogspot.com

No comments:

Post a Comment